<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya Ubanmu na cikin Sama,
 Dubi abokanmu,
 Sa musu duka albarkarka,
 Ka daɗa murnarsu.

[V2]
 2) Ka yafe musu laifofinsu,
 Ba su salamarka,
 Cece su daga wahalarsu,
 Ta wurin ikonka.

[V3]
 3) Ka gyara musu tunaninsu,
 Ka tsare harshensu,
 Tsabtad da dukan zukatansu,
 Cika ruhohinsu.

[V4]
 4) Daga makidai na Iblis,
 Daga duk ruɗewa,
 Bisa kowane kumamanci,
 Ka ba su nasara.

[V5]
 5) Kuma bari su gaskata fa
 A hannunka su ke.
 Bishe su kullum da ƙaunarka,
 Gama su naka ne.</lyrics>
<title>Ya Ubanmu Na Cikin Sama LW56</title>
<hymn_number>56</hymn_number>
</song>